9 Mayu 2021 - 14:01
Iran:Hilal Ahmar Ta Kasar Iran Zata Shigo Da Karin Alluran Riga Kafin Korona Miliyon Guda

Shugaban kungiyar bada agaji ta Hilal Ahmar ko Red Cross ta kasar Iran ya ci kungiyarsa tare da taimakon sauran kungiyoyin Hilal Ahmar ko Red Cross na wasu kasashen duniya za su taimaka mata ta shigo da Karin alluran riga kafin cutar korona miliyon guda a mako mai zuwa.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya nakalto Karim Himmati ya na fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, kungiyoyin Hilar Ahmar ko Red Cross na wasu kasashen duniya su na matukar taimkawa kungiyarsa don ganin an samar da alluran riga kafin cutar isassu a kasar Iran.

Kafin haka dai kungiyar ta shigo da alluran raga kafin cutar har miliyon biyu a makon da ya gabata.

Takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasar Iran dai ta hana kasar samun alluran riga kafi da kuma kayakin aikin kiwon lafiya don yaki da cutar korona a kasar daga kasashen waje.

342/